Featured
Majalisa Na Nazari Kan Ƙirƙirar Sabbin Jihohi 55 Da Ƙananan Hukumomi 278
Majalisar Dokoki ta Tarayyar Najeriya ta fara nazarin sabon shirin gyaran kundin tsarin mulki da zai iya kaiwa ga ƙirƙirar jihohi 55 sabbi da ƙananan hukumomi 278 a faɗin ƙasar. Wannan bayani ya fito ne daga mai magana da yawun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ismail Mudashir, a wata sanarwa da aka fitar daga Abuja a ranar Juma’a 24 ga Oktoba.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulki, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana hakan yayin buɗe taron hadin gwiwar majalisar dattawa da ta wakilai a Legas, inda ya jaddada cewa majalisar za ta samar da gyaran kundin mulki “mai amfani ga al’umma” kafin ƙarshen shekara.
Barau ya bayyana cewa aikin ya haɗa da kudurori 69, buƙatun kafa sabbin jihohi 55, buƙatun ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278, da buƙatun gyaran iyakoki biyu, bayan shafe shekaru biyu ana gudanar da tattaunawa da jama’a, ƙungiyoyi, da masana kan batun. Ya ce majalisar za ta yi ƙoƙarin tura sassan farko na gyaran zuwa majalisun dokoki na jihohi kafin ƙarshen shekara.
Sai dai masana harkokin siyasa sun yi gargadin cewa yawan buƙatun ƙirƙirar sabbin jihohi da ƙananan hukumomi na iya janyo sabbin rikice-rikice da rarrabuwar kai, kamar yadda aka gani a wasu yunƙurin baya da suka gaza cimma matsaya saboda bambancin ra’ayoyi da bukatun yankuna. Duk da haka, ana ganin wannan sabon yunƙuri na nuna sabuwar alamar daidaito da ƙuduri daga majalisar tarayya wajen sake fasalin tsarin mulkin ƙasar.
