Connect with us

Featured

Yunƙurin Juyin Mulki : Sojoji Sun Gano Naira Biliyan 45 a Asusun Hukumar Raya Yankin Neja Delta

Rundunar sojin Najeriya ta gano wasu makudan kudi da suka kai Naira biliyan 45 da ake zargin sun fito daga asusun Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), cikin binciken da ake yi kan zargin yunkurin juyin mulki a kasar. Rahotanni sun bayyana cewa kudin an bi da su zuwa wasu manyan mutane masu mukaman siyasa da kuma wasu sojoji da ake tsare da su bisa zargin hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A farkon watan nan, jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa an tsare hafsoshin sojoji 16 bisa zargin shirin juyin mulki, wanda aka danganta da soke bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai. Sai dai rundunar soji ta karyata wannan zargi, tana mai cewa ana bincikar hafsoshin ne saboda “laifin aikinsu,” ba saboda wani juyin mulki ba.

A yayin da binciken ke ci gaba, jami’an Hukumar Leken Asirin Sojoji (DIA) sun kai samame gidan tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon Ministan Man Fetur, Chief Timipre Sylva, inda suka kama kaninsa da direbansa. Wannan mataki ya tayar da jijiyoyin wuya a ofishin NDDC, inda ake binciken manyan jami’ai kan yadda kudaden suka fita da kuma wadanda suka amfana da su.

Sai dai Sylva ya musanta cewa yana da hannu cikin lamarin, yana mai cewa zarge-zargen siyasa ne da wasu ‘yan siyasa masu son gwamnati suka kirkira domin bata masa suna kafin zaben 2027. Kakakinsa, Julius Bokoru, ya bayyana cewa tsohon gwamnan yana kasar Birtaniya don duba lafiyarsa, kuma daga nan zai tafi taron kasuwanci a Malaysia. Rundunar soji ta sake jaddada cewa babu wani shirin juyin mulki a kasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet