Featured
Ba Za Mu Fasa Gudanar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomi a Neja Saboda Matsalar Ƴan Bindiga Ba – NSIEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja (NSIEC) ta bayyana cewa duk da matsalolin tsaro da ke addabar wasu yankuna na jihar, za a gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar 1 ga Nuwamba kamar yadda aka tsara. Shugaban hukumar, Jibril Imam, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da ake raba kayan zabe masu mahimmanci a Minna a ranar Alhamis. Ya ce an tanadi dukkan hanyoyin sufuri, ciki har da jiragen ruwa, domin tabbatar da cewa kayan zabe sun isa yankunan da ke bakin ruwa cikin lokaci.
Imam ya ce babu wani ɗan ƙasa da zai rasa damar kada kuri’a saboda matsalar ‘yan bindiga, inda ya bayyana cewa hukumar ta haɗa kai da hukumomin tsaro don kare lafiyar ma’aikata da masu kada kuri’a. Ya kuma tabbatar da cewa an tura ma’aikatan wucin gadi 5,249 zuwa mazabu da rumfunan zabe 4,950 da ke cikin mazaɓu 274 a dukkan kananan hukumomi 25 na jihar.
Shugaban ya ce an kammala dukkan shirye-shiryen da kundin tsarin mulki ya tanada kafin gudanar da zabe, kuma babu wata jam’iyya ko ƙungiyar lura da zabe da ta shigar da koke kan shirye-shiryen hukumar. Ya jaddada cewa NSIEC tana da cikakken shiri tare da jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya da gaskiya a lokacin zaben.
A ƙarshe, Imam ya bukaci ‘yan siyasa da su kiyaye yarjejeniyar zaman lafiya da suka rattaba hannu a kai, yana mai tabbatar da cewa hukumar za ta bai wa kowa da kowa damar fafatawa cikin adalci da lumana.
