Connect with us

Featured

Natasha Ta Gayyaci Akpabio Domin Buɗe Ayyuka a Mazabarta

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Jihar Kogi ta gayyaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da sauran sanatoci zuwa bikin kaddamar da ayyukan mazabarta a garin Ihima, Karamar Hukumar Okene, a ranar Lahadi. Wannan gayyata ta zo ne makonni bayan dawo dawowarta daga dakatarwar wata shida da majalisar ta yi mata.

An bayyana cewa gayyatar, wacce sanatar ta rattaba hannu kanta, ta nuna alamar sulhu tsakanin ita da Akpabio, bayan wani gagarumin rikici da ya barke tsakaninsu a watan Maris sakamakon yadda aka sake zaunar da ita a wani wuri daban a lokacin zaman majalisa. Akpabio, wanda ya karanta wasikarta a zauren majalisar, ya bayyana farin cikinsa tare da taya ta murna.

Tun bayan dawowarta, Natasha ta koma gudanar da aikinta a majalisa cikin natsuwa, har ta gabatar da gyaran kudirin dokar laifuffuka makon da ya gabata. Wannan sabon mataki nata ana kallonsa a matsayin hanyar gyara dangantaka da tabbatar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu a majalisar dattawa.

Masana siyasa sun bayyana wannan mataki a matsayin dabarar siyasa mai nufin sake gina amincewa, da kuma nuna cewa Natasha tana son mayar da hankali kan ci gaban mazabarta, ba rikici ba. Wannan lamari na iya zama sabon babi a siyasar Kogi da kuma a harkokin majalisar dattawa gaba ɗaya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet