Connect with us

Featured

Kotu ta Tsige Dan Majalisa Bayan Ya Sauya Sheƙa Daga PDP zuwa APC

Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisar wakilai na mazabar Gummi/Bukkuyum a Jihar Zamfara, Hon. Abubakar Suleiman Gummi, bayan da ya bar jam’iyyar PDP wadda a cikin ta ya samu nasarar zuwa majalisa inda ya koma APC. Alkalin kotun, Justice Obiora Egwuatu, ya yanke hukuncin cewa sauya shekar Gummi ya sabawa tanadin Sashe na 68(1)(g) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya haramta wa dan majalisa sauya jam’iyya idan babu rikici a cikin jam’iyyar da ta dauke shi.

Kotun ta umarci Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da ya cire Gummi a matsayin wakili a majalisarsa, tare da umartar INEC ta shirya sabon zabe cikin kwanaki 30 domin cike gurbin da ya bari. Alkalin ya kuma ce dan majalisar ya dawo da duk kudaden albashi da alawus-alawus da ya karɓa tun daga Oktoba 2024 zuwa ranar yanke hukuncin.

Justice Egwuatu ya soki yadda wasu ‘yan siyasa ke daukar sauya sheka a matsayin al’ada, yana mai kiran hakan “‘yan siyasa masu cin amanar jama’a.” Ya ce, “idan mutum ya fice daga jam’iyyar da ta kai shi mulki, bai da ikon daukar kuri’un jama’a zuwa wata jam’iyya.” Ya kara da cewa doka ce ke hukunta irin wannan ta hanyar kwace kujerar da dan siyasa ya samu ta jam’iyyar da ya bari.

Kotun ta kuma ba PDP da shugabanta na Zamfara, Jamilu Jibomagayaki, nasara kan karar da suka shigar, tare da laifin tarar N500,000 da za a biya su. Wannan hukunci ya sake jaddada cewa kotu ba za ta lamunci “karuwancin siyasa” ba, inda alkali ya yi kira ga ‘yan siyasa da su daina amfani da kujerun jama’a don biyan bukatun kansu.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet