Connect with us

Featured

Kotu Ta Ba da Umarnin Tsare Ƴan Ƙasashen Waje 21 Kan Zargin Cinikayyar Hodar Iblis

Kotun Tarayya da ke Lagos ta ba Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) umarnin tsare jirgin ruwa da fasinjoji 21 ‘yan ƙasashen waje, biyo bayan kama kilogiram 25.5 na hodar iblis (cocaine) a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa. An kama miyagun ƙwayoyin ne a ranar 6 ga Disamba, 2025, a cikin jirgin ruwa mai suna MV San Antonio, wanda ya iso daga ƙasar Brazil.

Bayan sauke kayan jirgin gaba ɗaya, jami’an NDLEA suka tsare kyaftin ɗin jirgin tare da sauran ma’aikata 20, bayan gano hodar iblis ɗin da aka ɓoye a cikin jirgin. Hukumar ta bayyana cewa ta nemi umarnin kotu ne bisa ka’idojin shari’a na ƙasa da ƙasa, domin a tsare jirgin da mutanen yayin da bincike ke gudana. Mai shari’a Justice Frida Nkemakonam Ogazi ta amince da buƙatar, tare da ba da umarnin tsare su na tsawon kwanaki 14 a matakin farko, kafin gurfanarwa.

Rahoton Kakaki24 ya nuna cewa Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya ce wannan nasara na nuna ƙudurin hukumar na tarwatsa hanyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa. Ya yaba wa jami’an rundunar Apapa, yana mai jaddada cewa NDLEA za ta ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin cikin gida da na waje domin kare Najeriya daga barazanar safarar miyagun ƙwayoyi. Shari’ar za ta ci gaba ne a ranar 29 ga Disamba, 2025.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino sitelerikavbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciograndpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet