Featured
Himma Radio 91.1FM Ta Sanya Yara 40 a Makaranta
Himma Radio 91.1FM, da ke Kano, ta kaddamar da shirin sanya yara 40 a makaranta karo na farko a Kafin Agur, karamar hukumar Madobi, jihar Kano.
Taron, wanda aka gudanar a harabar gidan rediyon a ranar Lahadi, 2 ga Nuwamba, 2025, ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar.
A yayin taron, an bai wa yara maza da mata su 40 cikakkun kayan makaranta — ciki har da uniform, jakunkuna, litattafai da kayan rubutu — domin su fara sabuwar rayuwa ta ilimi.
Cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Hakimin Madobi kuma Majidadin Kano, Alhaji Sale Musa Sale; Wakilin Gwamnan Kano, Alhaji Sale Musa Wailari; Wakilin Chairman na karamar hukumar Madobi, Hon. Nasir Sulaiman; da kuma Dr. Balabe Danlami Jazuli, wanda ya wakilci Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB). Haka kuma, Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Haruna Musa, ya halarta.
Da yake jawabi, Shugaban Himma Radio, Alhaji Ismail Yusuf Makwarari, ya bayyana cewa manufar shirin ita ce tallafa wa al’umma, musamman wajen ganin yara sun samu damar zuwa makaranta.
“Mun dauki wannan mataki ne domin taimaka wa wadannan yara da iyayensu, saboda noma na zamani ba zai yiwu ba sai da ilimi. Kuma tunda yawancin shirye-shiryen Himma Radio na da alaka da harkar noma, mun ga dacewar mu taimaka wajen sanya yara a makaranta domin su zama manoma masu ilimi a nan gaba,” in ji shi.
Ya ce Himma Radio za ta ci gaba da fadada irin wannan shiri zuwa sauran kananan hukumomi 44 na jihar Kano domin tabbatar da cewa ilimi ya karade ko’ina.
A nasa bangaren, Wakilin Gwamnan Kano, Alhaji Sale Musa Wailari, ya jinjinawa Himma Radio bisa wannan aiki na alheri, yana mai cewa ya yi daidai da manufofin gwamnatin Kano na bunkasa ilimi a fadin jihar.
“Gwamnatin Kano za ta yi hadin gwiwa da Himma Radio wajen fadada irin wannan shiri a dukkan fadin jihar, domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar zuwa makaranta,” in ji shi.
Shi ma Hakimin Madobi, Alhaji Sale Musa Sale, ya bayyana farin cikinsa da yadda aka gudanar da shirin a gundumarsa, inda ya yaba da kokarin Himma Radio tare da yin alkawarin bayar da dukkan gudunmawar da ta dace domin inganta bangaren ilimi a yankin.
Daya daga cikin iyayen yaran da aka sanya a makaranta, Sani Ismail, ya bayyana godiyarsa ga Himma Radio bisa wannan taimako.
“Mun dade muna son mu tura ’ya’yanmu makaranta, amma yanayin rayuwa bai ba mu dama ba. Yanzu ga dama ta zo, kuma wannan taimako zai taimaka musu su zama abin alfahari a gaba,” in ji shi cikin farin ciki.
Taron ya gudana cikin nishadi da girmamawa, inda Himma Radio 99.1FM ta tabbatar da jajircewarta wajen ci gaban al’umma, musamman a fannonin ilimi da noma.
