Connect with us

Addini

Samarin Tijjaniyya Sun Maka Gwamnan Kano a Kotu

Wani gungu na ƙungiyoyin addini da suka haɗa da Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam, Tijjaniyya Youth Enlightenment Foundation da wasu ƙungiyoyin Kadiriyya da Ashabul Kahfi, sun shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Jihar Kano, suna neman a tilasta wa Gwamnatin Kano ta gurfanar da Malam Abubakar Lawal, wanda aka fi sani da Lawan Triumph, bisa zargin aikata laifin cin mutuncin addini da ya shafi amfani da kafofin sadarwa.

Ƙungiyoyin sun ce akwai tanadi a Dokar Shari’ar Jihar Kano da Dokar Rigakafin Laifukan Intanet ta 2024, wanda ke wajabta wa gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki mataki idan an aikata irin wadannan laifuka, amma sun yi zargin cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kwamishinan ‘yan sanda, da kwamishinan shari’a sun gaza cika wannan nauyi.

A cikin ƙarar, ƙungiyoyin sun nemi kotu ta bayar da umarnin tilasta gwamnati ta fara shari’a, tare da neman a duba ko akwai kuskuren doka ko wasa da alhakin gwamnati wajen kin gurfanar da wanda ake zargi, duk da korafe-korafen da aka mika tun farko.

Wannan ƙara na zuwa ne a dai-dai lokacin da al’amurran da suka shafi cin zarafin addini a shafukan sada zumunta ke ƙara jawo muhawara mai zafi a Kano. Masu ƙarar na fatan hukunci zai zama darasi ga masu amfani da intanet ta hanyar da ka iya tada fitina ko rikici tsakanin al’ummomi. Gwamnatin Kano da sauran wadanda aka yi ƙarar dai ba su fitar da martani a hukumance ba tukuna.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet