Connect with us

Featured

Yara Biyu Sun Rasu Sakamakon Faɗawa Rijiya a Kano

Wasu yara biyu sun rasa rayukansu a cikin kwanaki biyu a sassa daban-daban na jihar Kano bayan faɗawa cikin rijiyoyi. Lamarin ya faru ne a unguwar Dandishe Tsamiyar Goodluck da kuma ƙauyen Kashirmo na karamar hukumar Dawakin Tofa.

A Dandishe, yaro mai suna Ahmad Abdurashid, mai shekara shida, ya faɗa rijiya da misalin ƙarfe 10:02 na safe a ranar Laraba. Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce ta sami kiran gaggawa, inda tawagar ta isa wurin cikin gaggawa, amma duk da kokarin da aka yi, an ciro Ahmad ne a mace, sannan aka miƙa gawarsa ga mahaifinsa.

A wani lamarin makamancin haka, wata yarinya mai kimanin shekara takwas ta faɗa rijiya a kauyen Kashirmo kusa da Sarkakiya a karamar hukumar Dawakin Tofa a ranar Talata. Tawagar ceto ta tura jami’ai zuwa wurin, sai dai ba su samu nasarar ceto yarinyar daga ruwan ba har sai jikinta ya mutu.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa an fara bincike kan dalilan faruwar waɗannan abubuwa, tare da yin kira ga jama’a su rufe rijiyoyinsu da kyau, kana su kauce wa barin rijiyoyi a buɗe musamman a yankunan da yara ke yawan wasa. Wannan na zuwa ne a yayin da irin waɗannan haɗurra ke ƙara faruwa a wasu yankuna na jihar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet