Connect with us

Featured

Yawan Masu Amfani da Wutar Lantarki Ya Ƙaru a Najeriya

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta bayyana cewa yawan masu amfani da wutar lantarki a fadin kasar ya karu daga miliyan 11.89 a watan Yuli zuwa miliyan 11.96 a watan Agusta 2025. Rahoton ya nuna cewa daga cikin wadannan, miliyan 6.58 ne kawai ke amfani da mita.

NERC ta bayyana cewa an kara wa abokan huldar wutar lantarki mita guda 70,888 a watan Agusta, yayin da watan Yuli aka kara mita 76,783. Wannan karuwar tana nuna kokarin kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) wajen tabbatar da adalci a lissafin kudin wuta da inganta amincewar masu amfani. A jerin kamfanonin da suka fi samun nasarar sanya mita akwai Eko, Ikeja, da Abuja DisCos, wadanda suka kai kaso 84.25, 84.83, da 73.92 cikin 100 na masu amfani da mita, bi da bi.

A wani bangare, NERC ta sanar da cewa a farkon shekarar 2025, kamfanonin rarraba wuta takwas sun samu tarar fiye da Naira miliyan 628 saboda saba ka’idojin iyakar amfani da wuta ga wadanda ba su da mita. Hukumar ta umurci kamfanonin su biya masu amfani da wutar da abin ya shafa diyya.

Haka kuma, a karshen kwata na biyu na 2025, an sanya mita guda 225,631 a kasar, karuwa mai kashi 20.55 daga mita 187,161 da aka sanya a kwata na farko. Daga cikin wadannan, mita 147,823 (65.52%) an sanya su ne ta shirin Meter Asset Provider, 65,315 ta Meter Acquisition Fund, 12,259 ta hanyar vendor financing, sannan 234 ta DisCo-financed scheme.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet