Featured
Kashi 1 Cikin 3 Na Ƴansandan Najeriya Gadin Ƴan Siyasa Suke Yi – EU
Wani sabon rahoto daga Hukumar EU mai Kula da Batutuwan Gudun Hijira ya bayyana cewa fiye da jami’an ‘yan sanda 100,000 a Najeriya ne ke aiki wajen kare ‘yan siyasa da wasu manyan mutane (VIP), maimakon su tsaya kan aikin tsaro ga al’umma. Rahoton ya nuna cewa adadin jami’an ‘yan sanda a Najeriya yana kusan 371,800, alhali yawan jama’ar kasar ya kai mutane 236.7 miliyan, wanda ke haifar da babbar gibin tsaro a ƙasar.
Rahoton ya ce wannan karancin ya jawo jinkiri wajen amsawa kiran gaggawa, tare da barin wasu yankuna ba tare da jami’an tsaro ko shinge na kariya ba. Haka kuma ya nuna cewa rashin isassun kayayyakin aiki da cin hanci a wasu bangarorin na kara lalata sha’anin tsaro. Har ila yau, rahoton ya ce rashin ingantaccen hukunci kan jami’an da suka karya doka yana haifar da matsaloli irin su tsare mutane ba bisa ka’ida ba, karɓar rashawa da amfani da karfi fiye da kima.
A baya, Shugaban ‘Yan Sanda na Kasa, Kayode Egbetokun, ya umarci a janye jami’an Mobile Police daga gadin VIP, amma rahoton ya nuna cewa umarnin bai yi tasiri sosai ba. Haka zalika, a watan Agusta 2025, Hadiza Bala-Usman, mai ba Shugaban Kasa shawara kan manufofi, ta yi kira da a dakatar da wannan dabi’a.
Ta jaddada cewa idan wani babban mutum ya na buƙatar yawan masu tsaro, ya kamata ya biya kamfani mai zaman kansa, ba ya dora wa gwamnati nauyi ba. Ta kuma yi kira da a gyara dokar ‘Yan Sanda, domin ‘yan sanda su koma mayar da hankali kan tsarin tsaron ƙasa, ba gadin mutanen da suka mallaki kudi ko mukami ba.
