Connect with us

Featured

Ƙungiyar Ƴan Jaridun Yanar Gizo a Jihar Kano Ta Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Mambobinta

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana jaridar yanar gizo a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen isar da saƙon gwamnati cikin gaggawa da inganci, tare da kudurin ƙara ƙarfafa haɗin kai da masu aikin jarida na intanet. Wannan jawabi ya fito ne daga Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamna Abba Kabir Yusuf, Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, yayin taron horaswa na yini ɗaya da Kano Online Media Chapel ta shirya a ranar Talata 18 ga Nuwamba, 2025, a Ma’aikatar Sufuri da ke Goron Dutse. Ya kuma sanar da tallafin Naira miliyan biyu domin gyaran ofishin ƙungiyar, yana mai jaddada muhimmancin kafafen yanar gizo a wannan zamani na fasahar Artificial Intelligence (AI).

A nasa bangaren, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Comrade Abdullahi Waiya, ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da goyon bayan duk wani shiri da zai inganta ƙwarewar ‘yan jaridar yanar gizo, tare da tabbatar da cewa gwamnati na kallon su a matsayin muhimman abokan aiki. Haka kuma shugaban NIPR reshen Kano, Aliyu Yusuf, ya bayyana taken taron a matsayin na zamani, ganin yadda fasahar AI ke sauya tafiyar aikin jarida cikin sauri.

Tun da farko, Shugaban Kano Online Media Chapel, Comrade Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya gode wa mahalarta taron tare da bayyana matakan da ƙungiyar ta ɗauka tun bayan kafuwarta, ciki har da tsaftace tsarin aikin jaridar yanar gizo da bude asusun ƙungiya domin inganta aiki. Ya kuma lissafo kalubalen da suke fuskanta, musamman ƙarancin ofishi da rashin motar aiki, tare da neman tallafin babbar mota domin sauƙaƙa ayyukan jarida a fadin jihar.

Taron, wanda ya samu halartar jami’an tsaro, ‘yan jarida daga manyan gidajen labarai ciki har da KAKAKI24, da masana fannin sadarwa, ya ƙare da gabatar da maƙala ta musamman da Farfesa Rukayya Yusuf Aliyu ta Jami’ar Bayero ta yi kan muhimmancin rungumar sabbin fasahohi domin ci gaba da kasancewa a sahun gaba a duniyar jaridar zamani.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet