Connect with us

Featured

Arewa Connect Movement Ta Bayyana Alhininta Game Da Sace Ɗalibai 150 a Neja

21/11/2025 – 10:00am

 

Cike da tashin hankali da alhini, al’umma a Najeriya sun shiga damuwa bayan wasu batagari suka sace malamai da dalibai kusan 150 daga wata makaranta a jihar Neja. Wannan mummunan lamari ya sake tayar da hankula, musamman kasancewar bai daɗe da faruwar sace-sacen dalibai mata su 25 a jihar Kebbi ba, har yanzu kuma babu labarin su.

A yayin da ake ci gaba da tofa albarkacin baki kan wannan hari, masana tsaro da al’ummar gari na ganin wannan abu babban kalubale ne ga gwamnati da hukumomin tsaro, duba da yadda irin wannan ta’ada ke cigaba da faruwa babu ƙakkautawa. A cewarsu, lokaci ya yi da gwamnati za ta sauya salo, ta ɗauki tsattsauran mataki domin fatattakar waɗannan miyagu gaba ɗaya.

Kungiyar Arewa Connect Movement ta bayyana damuwarta, tana kuma kira ga al’ummar Najeriya da su tashi tsaye wajen kawo ƙarshen wannan masifa. A cewar kungiyar, ya zama dole al’umma da gwamnati su haɗa kai domin kare rayuka da makomar yaran da ake gaba da su. Kakaki24 ta tattaro cewa kungiyar ta bayyana cewa ci gaba da zubar da hawaye ba zai warware matsalar ba, sai tsayuwar daka da buri na bai-daya.

Daga ƙarshe, kungiyar ta miƙa sakon ta’aziyya ga gwamnatin tarayya, jihohin Kebbi da Neja, iyayen waɗanda abin ya shafa da sauran al’umma. Ta kuma yi addu’ar Allah Ya kawo ɗauki cikin ggaggawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet