Connect with us

Featured

Obi Ya Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Hukuncin Da Aka Yankewa Nnamdi Kanu

Dan takarar shugaban kasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, ya bayyana rashin amincewarsa da hukuncin da aka yanke wa shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, inda kotun tarayya ta Abuja ta yankewa Kanu hukuncin daurin rai-da-rai. Obi, wanda ya yi rubutu a shafinsa na X ranar Asabar, ya ce wannan hukunci “tsohon al’amari ne da ya samo asali daga gazawar shugabanci” musamman a wannan lokaci da Najeriya ke fama da tsananin talauci, tsaro, da rashin ingantaccen jagoranci.

A cewar Obi, gwamnati ta yi kuskure tun daga matakin farko na kama Kanu, tsare shi na dogon lokaci, har zuwa wannan hukunci. Ya ce matsalolin da Kanu ya dinga dagawa gwamnati ba “abubuwa ne marasa yiwuwa ba,” don haka ya kamata gwamnati ta yi amfani da tattaunawa, sassauci, da hanyar siyasa wajen warware matsalar. Obi ya jaddada cewa a ƙasashe masu ci gaba, irin wannan rikici kan buƙaci hanyoyin sulhu maimakon takura.

Obi ya gargadi cewa hukuncin na iya kara ta’azzara rashin jituwa a ƙasar, ganin halin da ake ciki na tsadar rayuwa da rashin tsaro. A cewarshi, shugabanci ba wai bin doka kaɗai ba ne, har da neman mafita ta siyasa domin tabbatar da zaman lafiya. Ya shawarci shugaban kasa, majalisar koli ta ƙasa da dattawan ƙasar su shiga ciki domin samar da hanyar sulhu da sassaucin siyasa da zai kawo ƙarshe ga wannan rikici tare da bai wa ‘yan Najeriya kwanciyar hankali.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet