Connect with us

Featured

Da Ɗumi-ɗumi : Sojoji Sun Yi Juyin Mulki a Guinea-Bissau

Jami’an soji a Guinea-Bissau sun ayyana cewa sun karɓi cikakken iko a kasar bayan harbe-harbe da aka ji a birnin Bissau, tare da rahotannin kama shugaban ƙasa Umaro Sissoco Embaló. Sojojin sun bayyana a gidan talabijin na ƙasa inda suka sanar da dakatar da tsarin zaben da aka gudanar a ranar Lahadi, wanda ya haifar da takaddama bayan hana dan takarar adawa tsaya wa takara, duk da cewa ana sa ran sanar da sakamakon zaben a ranar Alhamis kuma Embaló da abokin hamayyarsa Fernando Dias sun yi iƙirarin nasara.

 

A sanarwar da Janar Denis N’Canha, shugaban sojojin fadar shugaban ƙasa, ya karanta, sojojin sun bayyana rufe dukkan iyakokin ƙasar tare da umartar jama’a da su kwantar da hankali. Kakaki24 ta tattaro cewa baya ga shugaban ƙasa, an kuma kama hafsan sojojin fadar shugaban ƙasa da wasu ministocin gwamnati, abin da ya kara tayar da hankula a yammacin Afirka, yankin da ke ci gaba da fama da juyin mulki a wasu kasashe kamar Mali, Burkina Faso da Nijar.

 

Masu nazari na ganin rikicin siyasa da rashin amincewa da sakamakon zabe na iya kara jefa Guinea-Bissau cikin matsanancin hali, yayin da ake jiran matakin da kungiyoyin yanki irin su ECOWAS za su dauka. Har yanzu babu cikakken bayani game da inda aka ajiye Embaló ko makomar gwamnatin sa, yayin da kasashen duniya ke kira da a mutunta doka, tabbatar da zaman lafiya da kiyaye ‘yancin zaben jama’a.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet