Connect with us

Featured

2027: Takarar Shugaban Ƙasa Nake So Ba Mataimaki Ba – Amaechi

Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya karyata rade-radin cewa zai iya zama mataimakin Atiku Abubakar ko wani dan takarar shugaban kasa a 2027. Amaechi ya bayyana cewa shi kansa zai tsaya takarar shugaban kasa, ba ya kuma sha’awar zama mataimaki ga kowane ɗan siyasa.

Wannan martani nasa ya biyo bayan batun da Dele Momodu ya yi, inda ya ce idan Peter Obi bai amince ba, Atiku na iya ɗaukar Amaechi saboda irin rawar da ya taka wajen kawo Buhari mulki a 2015. Sai dai Amaechi ta bakin mai magana da yawunsa, David Iyofor, ya ce ba ya cikin wata tattaunawa da ta shafi tikitin hadaka ko zama abokin takara.

Kakaki24 ta ruwaito cewa Amaechi ya dage cewa yankin Kudu ne ya kamata ya samar da shugaban kasa a 2027, don haka yake neman tikitin jam’iyyar ADC domin tsayawa takara. Ya ce ba ya son a riƙa saka sunansa cikin duk wani lissafi da ya shafi mataimakin shugaban kasa, domin burinsa shi ne zama shugaban Najeriya.

Amaechi, wanda ya nemi takarar shugabancin Najeriya a APC a 2023 kafin daga baya ya koma ADC, ya ce ya himmatu wajen samun tikitin jam’iyyar don jan takarar 2027. Ya gargadi ‘yan siyasa da su daina danganta shi da duk wata tattaunawar da ba ya ciki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet