Connect with us

Featured

Dokar Hana Yara Amfani Da Shafukan Facebook, TikTok Ta Fara Aiki a Australia

Kamfanin Meta ya fara goge shafukan matasa ‘yan ƙasa da shekaru 16 a Ostiraliya daga Instagram, Facebook da Threads. Wannan na zuwa ne mako guda kafin sabuwar dokar kasar ta fara haramta wa matasa amfani da kafafen sada zumunta. An riga an sanar da masu shekaru 13 zuwa 15 cewa za a rufe shafukansu tun daga yau.

 

Rahotanni sun nuna cewa kusan masu amfani 150,000 a Facebook da 350,000 a Instagram za su shiga cikin waɗanda wannan mataki zai shafa. A bangaren Threads kuwa, ba za a iya amfani da shi kai tsaye ba sai dai ta hanyar Instagram. Wannan dai shi ne karo na farko da wata ƙasa ta kafa irin wannan doka ta takaita matasa daga kafafen sada zumunta.

 

A cewar bayanai da Kakaki24 ta tattaro, dokar ta Ostiraliya za ta fara aiki ne daga 10 ga Disamba 2025. Za a rika cin tarar kamfanoni har zuwa A$49.5m idan suka kasa hana matasa ƙasa da 16 amfani da dandalan. Meta ta bukaci gwamnati ta mayar da wajibi ga rumbun manhajoji su tabbatar da shekaru kafin a sauke kowace manhaja.

 

Wadansu manyan kafafen sada zumunta da dokar ta shafa sun haɗa da YouTube, X, TikTok, Snapchat, Reddit, Kick da Twitch. Masu sharhi na cewa dokar na iya zama abin koyi ga sauran ƙasashe, ganin yadda matsalolin tsaro da tsangwama ta yanar gizo ke ƙaruwa a tsakanin matasa a fadin duniya.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet