Connect with us

Featured

Maganganun Salah Zasu Ɓata Masa Tarihinsa a Liverpool – Rooney

Tsohon tauraron Manchester United, Wayne Rooney, ya yi gargadi cewa Mohamed Salah na “na iya lalata kyakkyawan tahirinsa ” a Liverpool bayan ya zargi kulob ɗin da “jefa shi cikin matsala” tare da nuna rashin jituwa tsakaninsa da kocin Liverpool, Arne Slot. Wannan ya zo ne bayan Salah ya koka kan ƙarancin damar da ake ba shi a wasa, yana zargin wasu a kulob ɗin da neman ɗora masa alhakin koma-bayar da kungiyar ke fuskanta.

Rooney ya ce lokaci ya yi da Arne Slot zai tabbatar da ikonsa ta hanyar cire Salah daga jerin ’yan wasan da za su fuskanci Inter Milan a Champions League ranar Talata, da kuma wasan gida da Brighton a karshen mako. Ya bayyana wannan a sabon shirin sa na podcast inda ya ce, “Da ni ne, babu makawa sai na hana shi tafiya tare da tawaga. Abin da ya faɗa ba zai taba karɓuwa ba.”

A cewar Rooney, dole ne Salah ya gyara al’amuransa da Arne Slot ko kuma ya yi watsi da Liverpool gaba ɗaya, domin rikicin zai iya lalata duk nasarorin da ya gina tun zuwansa daga Roma a 2017. Kakaki24 ta tattaro cewa Rooney ya yi tambaya kan dalilin da ya sa Salah ya fito fili yana magana a bainar jama’a, yana mai cewa hakan “na rusa tarihin da ya gina a cikin shekaru.”

Rooney ya ƙara da cewa abin takaici ne ganin Salah ya yi hanyar batar da mutuncinsa a wajen magoya baya da kulob ɗin da ya yi fice a ciki. Tun farko PUNCH Online ta ruwaito yadda Salah ya nuna takaici game da yadda ake rage masa dama a wasa, yana zargin wani a kulob da neman ɗora masa laifi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet