Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Buƙaci Ƴan Jaridu Su Riƙa Taka-Tsantsan Wajen Bayar Da Rahoto Kan Tsaro a Jihar

Gwamnatin Kano ta yi kira ga kafafen yada labaran yanar gizo, da su rika taka-tsantsan wajen wallafa duk wani rahoto, musamman kan sha’anin tsaro, domin kare martabar al’ummar jihar.

Wannan kira ya fito ne daga Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, a yayin taron manema labarai da ya gudana ranar Alhamis, 11 ga Disamba, 2025, a dakin taron Ma’aikatar Yada Labarai da ke Sakatariyar Audu Bako, Kano.

Waiya ya ce akwai bukatar ’yan jarida na intanet su dinga zurfin nazari kafin wallafa labarai masu nasaba da tsaro, domin yaɗa bayanan da ba su da inganci kan iya haifar da tashin hankali ko ƙarin matsaloli a jihar.

Ya ce akwai wata kafar yanar gizo da ta wallafa labarin karya kan cewa Kano cike take da ’yan ta’adda, yana mai cewa irin hakan ba kawai ya saba ƙa’idoji ba, har ma yana cutar da zaman lafiyar mutane.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati na ganin irin goyon bayan da kafafen labarai ke bayarwa — ciki har da rahotannin Kakaki24 — wajen faɗakar da jama’a da kawar da jita-jita.

Ya ƙara da cewa wannan haɗin kan ne zai taimaka wajen dakile matsalar tsaro, tare da tabbatar da cewa rahotanni suna fita cikin kwarewa da gaskiya.

A nasa bangaren, shugaban Kano Online Media Chapel, Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya yi alkawarin cewa mambobinsu za su cigaba da aiki da doka, tare da kaucewa rubuce-rubucen da ka iya tada jijiyoyin wuya.

Ya kuma ce kafafen yanar gizo suna da rawar da za su taka wajen samar da zaman lafiya.  Mambobin kungiyar sun yaba da wannan taro da ya basu damar fahimtar irin rawar da ya kamata su taka wajen tsaron jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet