Featured
Dangote Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa 699
A ranar Alhamis 11 ga Disamba 2025, kamfanin Dangote Refinery ya sake rage farashin man fetur (PMS) daga N828 zuwa N699, raguwar da ta kai N129, wato kashi 15.58%. Wannan bayanin ya fito ne daga sabbin alkaluman kasuwa da shafin Petroleumprice.ng ya wallafa, tare da tabbatarwar jami’in kamfanin ga jaridar PUNCH.
Wannan saukar farashi shi ne karo na 20 cikin wannan shekara da kamfanin ya sanya sabon tsari, kuma ya zo ne mako guda bayan taron da Alhaji Aliko Dangote ya yi da Shugaba Bola Tinubu a Abuja, inda ya ce kamfanin nasa ya kuduri niyyar tabbatar da farashin man da zai zama mai araha.
Ya ce raguwar farashin man na da alaƙa da ƙaruwar samarwa, kasancewar sauye-sauyen farashin man duniya da kuma raguwar fasa-kwari a kan iyakokin ƙasar. Ya jaddada cewa kamfanin bai fito domin neman riba cikin gaggawa ba, domin wannan jarin na da tsawon lokaci kafin ya dawo.
Biyo bayan gangamin Dangote, wasu manyan rumbunan ajiya sun bi sawu, ciki har da Sigmund Depot da ya rage farashinsa zuwa N824, Bulk Strategic da TechnoOil, tare da AA Rano, NIPCO da Aiteo da suka yi gyara kaɗan. Wannan mataki ya nuna yadda kasuwa ke amsa sabon farashin da Dangote ya fito da shi.
