Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Haramtawa Ɗaliban SS2 Zana Jarrabawar Kammala Sakandire
Gwamnatin Tarayya ta haramta karɓa ko matsar da ɗalibai zuwa aji uku na Senior Secondary School (SS3) a dukkan makarantu na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta fito ne a ranar Lahadi, 14 ga Disamba, 2025 da misalin ƙarfe 11:25 na safe, daga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, domin rage yawaitar maguɗin jarrabawa.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai ta ma’aikatar, Boriowo Folasade, ta sanya wa hannu, ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon ƙaruwa da ake samu na maguɗin jarrabawa, ciki har da amfani da “special centres” a jarrabawar waje, abin da ke tauye martaba da sahihancin tsarin ilimi na Najeriya.
Ma’aikatar ta bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga shekarar karatu ta 2026/2027, inda za a takaita karɓa da canja ɗalibai zuwa SS1 da SS2 kawai. A cewar rahoton Kakaki24, wannan mataki na nufin hana motsa ɗalibai a ƙarshen karatunsu domin neman fa’ida a jarrabawa, tare da tabbatar da ci gaba da daidaito a koyarwa da sa ido kan karatu.
Gwamnatin Tarayya ta umarci masu makarantu, shugabanni da masu kula da makarantu da su bi wannan doka ba tare da ƙetarewa ba, tana mai gargaɗin cewa duk wanda ya karya dokar zai fuskanci hukunci bisa ƙa’idojin ilimi.
Hakan na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na kare martabar jarrabawar ƙasa, tabbatar da adalci, da dawo da amincewa ga tsarin ilimi a Najeriya.
