Connect with us

Featured

Gezawa : Tun Da Nake Ban Taɓa Ganin Sama Da Ɗalibai 10 Sun Zo Makaranta a Rana Ba – Shugaban Makaranta 

Danmadanho, Kano – Makarantar Government Secondary School (GSS) Danmadanho, Gezawa, wacce aka kafa a shekarar 2008, na fuskantar babban kalubale na rashin zuwan dalibai. Duk da cewa makarantar na da dalibai 280 kuma tana da malamai uku da ke koyar da darussa 9, amma rashin zuwan ɗaliban ya jefa makarantar cikin mawuyacin hali.

Mukaddashin shugaban makarantar, Malam Yahya Isa, ya bayyana wa Kakaki24 cewa, babban dalilin karancin dalibai shi ne yanayin garin. “Gari ne na manoma, kuma kusa da Kwari. Yaran da suka kai shekaru na sakandare yawanci sun fara girma, shiyasa suke tafiya noma ko neman kudi. A sakamakon haka, ba sa zuwa makaranta,” in ji shi. Ya kara da cewa, a tsawon zamansa a makarantar bai taba ganin dalibai sama da goma sunje makarantar a rana guda ba.

A kan tambayar ko karancin malamai ko rashin jajircewar su ke haifar da wannan matsala, Malam Yahya Isa ya ce, “Ba haka bane. Malamanmu sun yi iya kokarinsu wajen jawo hankalin iyayen daliban, amma duk da haka, yaran ne kawai ba sa zuwa.”

Makarantar ta samu tallafi daga Agile a baya-bayan nan inda aka gina musu burtsatse, kuma a zahiri basu da wasu bukatu na musamman daga gwamnati. Duk da haka, makarantar na rokon mahukunta da su dauki mataki cikin gaggawa don ganin an shawo kan wannan matsala, domin yaran yankin su samu ilimi yadda ya kamata, ta yadda zasu samu kyakkyawar makoma a nan gaba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantpusulabetvdcasinograndpashabetmarsbahisholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetmatadorbetonwinimajbetmatbetmatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantsahabetsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet