Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Bata Samu Kuɗaɗen Shigar Da Ta Yi Hasashen Samu Ba – Ministan Kuɗi

Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙin Najeriya, Wale Edun, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta cimma burinta na samu kuɗaɗen shiga a shekarar 2025 ba, sabanin abin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya faɗa a baya. Edun ya ce daga cikin Naira tiriliyan 40.8 da aka tsara za a samu, gwamnati ta samu kusan Naira tiriliyan 10.7 ne kawai zuwa yanzu, lamarin da ke nuna babban gibi a kuɗaɗen shiga.

 

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da kwamitocin Majalisar Wakilai kan Kuɗi da Tsare-tsaren Ci gaban Ƙasa, yayin nazarin shirin kashe kuɗaɗe na 2026 zuwa 2028 (MTEF/FSP). Wannan dai ya zo ne bayan Shugaba Tinubu ya shaida wa wasu baƙi a Fadar Shugaban Ƙasa cewa Najeriya ta riga ta cimma burin kuɗaɗen shigarta tun watan Agusta, tare da rage dogaro da rance.

 

Sai dai Edun ya danganta gaza cika burin ne da raunin kuɗaɗen shiga daga man fetur da iskar gas, musamman harajin ribar man fetur da na kamfanoni. Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta karɓi rancen kusan Naira tiriliyan 14.1 a shekarar don cike gibin da aka samu, abin da ke ƙara tayar da damuwa kan dorewar tattalin arziƙin ƙasar.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet