Featured
Canada Ta Kori Ƴan Najeriya 366 Daga Ƙasar
Kasar Canada ta kori ƴan Najeriya 366 daga watan Janairu zuwa Oktoban 2025, yayin da hukumomin shige da fice ke ƙara tsaurara matakan aiwatar da dokokin ƙaura, matakin da ba’a ga irinsa ba a cikin shekaru fiye da goma, kamar yadda bayanai daga Hukumar Kula da Iyakokin Canada (CBSA) suka nuna.
Rahoton ya kuma bayyana cewa ’yan Najeriya 974 na cikin jerin mutanen da ake shirin korarsu daga kasar, inda Najeriya ta zo ta tara a cikin kasashe goma da aka fi kora, sannan ta biyar a jerin mutanen da ke jiran a kore su. Bayanai sun nuna cewa adadin ƴan Najeriya da ake kora ya ragu a shekarun baya kafin ya ƙaru a 2025.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Canada ke ƙara tsananta matakan shige da fice, inda ake korar kusan baki 400 a kowane mako. Dokokin kasar sun tanadi nau’o’in umarnin korar baki uku, kuma galibin wadanda ake korar su ’yan neman mafaka ne da aka ƙi amincewa da bukatunsu, yayin da laifuka ke wakiltar kaso kaɗan daga cikin adadin.
