Featured
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Jami’ai
Rundunar Sojin Nijeriya ta buɗe shafin shiga Direct Short Service Commission (DSSC) Course 29/2026). Rundunar ta gayyaci ’yan Nijeriya da suka cancanta su nemi shiga domin zama hafsoshi a sassa daban daban na musamman.
Sanarwar ta ce an buɗe shirin DSSC ga fararen hula da kuma jami’an soja masu aiki da ke da ƙwarewa ta musamman. Za a tura waɗanda suka yi nasara zuwa sassa daban-daban na rundunar domin tallafa wa harkokin tsaro da kare ƙasa.
An bayyana cewa neman aikin kyauta ne, kuma za a yi ta yanar gizo daga 7 ga Janairu zuwa 4 ga Fabrairu, 2026. Masu sha’awa su nemi shiga ta shafin recruitment.army.mil.ng, ko su tuntubi layukan taimako na rundunar domin ƙarin bayani.
