Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Shiryawa Ƴan Jaridar Yanar Gizo Taron Bita Na Kwanaki Biyu a Jigawa

Gwamnatin Jihar Kano ta shirya taron horaswa na kwana biyu ga masu wallafa labarai ta yanar gizo, domin ƙara inganta ƙwarewa, ɗabi’a da ingancin aikin jarida a zamanin dijital. Taron wanda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta shirya, na gudana ne a birnin Dutse na Jihar Jigawa.

Da yake buɗe taron a ranar Laraba 14 ga Janairu, 2026, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana kafafen yaɗa labarai na yanar gizo a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen tafiyar da dimokuraɗiyya da wayar da kan al’umma. Ya ce dole ne aikin jaridar yanar gizo ya kasance bisa gaskiya, ƙwarewa da bin ƙa’idoji domin kare amincewar jama’a.

Kwamared Waiya ya jaddada cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na da cikakken ƙuduri wajen kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da bunƙasa aikin jarida, musamman ganin yadda fasahar zamani, ICT da basirar wucin-gadi (AI) ke ƙara tasiri a harkar yaɗa labarai.

A jawabansu, Shugaban NUJ reshen Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Dederi, da Shugaban Ƙungiyar Kafafen Yanar Gizo, Kwamared Abubakar Dangambo, sun yaba wa gwamnatin jihar bisa shirya taron. Sun ce taron zai taimaka wajen gina ‘yan jarida masu ɗabi’a, sanin doka da kuma aiki bisa ƙa’idar sana’a.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet