Connect with us

Featured

Rundunar Ƴansandan Kano Ta Tabbatar Da Kisan- gillar Uwa Da Ƴaƴanta 6 a Dorayi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar wani mummunan kisan gilla a unguwar Dorayi Chiranchi, inda aka kai hari gidan Haruna Bashir da misalin karfe 12:10 na rana a ranar Asabar, 17 ga Janairu, 2026. Rahoton ya nuna cewa Fatima Abubakar mai shekaru 35 da ’ya’yanta shida sun rasa rayukansu bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidansu tare da kai musu hari da makamai masu hatsari.

Bayan samun kiran gaggawa, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya bayar da umarnin gaggawa inda aka tura tawagar ’yan sanda karkashin jagorancin DCP Lawal Isah Mani, domin duba lamarin da daukar matakan farko na tsaro da bincike.

Rahotanni da Kakaki24 ta samu sun ce an kwashe gawarwakin wadanda abin ya shafa zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu. Haka kuma, ACP Wada Jarma na Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) ya samu umarnin jagorantar cikakken bincike domin gano tare da cafke wadanda suka aikata wannan ta’asa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu, al’ummar Dorayi Chiranchi da daukacin jama’ar jihar, tare da tabbatar da kudurinta na ganin an hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika, domin tabbatar da tsaro da adalci a Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet