Featured
Najeriya Ta Karɓi Ƴan Gudun Hijira 153 Daga Jamhuriyar Nijar
Najeriya ta karɓi ƴan gudun hijira 153 daga Jamhuriyar Nijar, a wani yunkuri na tabbatar da dawowarsu cikin aminci da mutunci. Ofishin hukumar NEMA reshen Kano ne ya karɓe su tare da haɗin gwiwar NRC, SEMA da rundunar tsaro ta NSCDC.
Ƴan gudun hijirar sun sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 12:50 na tsakar daren Talata, ta jirgin Sky Mali Airline. Bayan kammala rajista da hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS), an kai su makarantar horarwar hukumar domin bincike da tantancewa.
An gudanar da tantancewar a ranar 27 ga Janairu, 2026, inda aka gano akwai maza manya 46, mata manya 37, yara maza 38 da yara mata 32. Hukumomi sun bayyana cewa aikin ya gudana cikin tsari da nasara, ba tare da fuskantar wata babbar matsala ba.
