Featured
Tinubu Ya Nemi Haɗin-kan Ƙasashen Yammacin Afirka Domin Daƙile Matsalar Tsaro
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi kira da a farfaɗo da rundunar tsaro ta yankin Yammacin Afirka domin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen yaki da matsalar rashin tsaro a yankin da Sahel. Ya kuma bukaci ƙasashen yankin su yi amfani da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) da ke Abuja a matsayin cibiyar tattara bayanan sirri.
An bayyana matsayar Tinubu ne ta bakin Ƙaramar ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, a taron tsaro da aka gudanar a Accra, Ghana, daga 29 zuwa 30 ga Janairu, 2026. Shugaban ya jaddada kudirin Najeriya na kare zaman lafiya da tsaro, tare da kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe domin shawo kan matsalar tsaro a Sahel.
Tinubu ya kuma yi gargadi kan yadda ‘yan ta’adda ke amfani da kafafen yanar gizo wajen yaɗa ƙarya da rikitarwa, yana mai cewa hakan na barazana ga tsaro. Ya bukaci ECOWAS da ƙasashen AES su rage tashin hankali tare da kafa tsari na bai daya da zai kare muradun tsaro da tattalin arzikin yankin.
