Featured
Kano : PWAN Ta Horas da ’Yan Jarida Kan Dokar ’Yan Sanda ta 2020
Ƙungiyar Rule of Law and Empowerment Initiative (PWAN) tare da tallafin FCDO ta shirya taron yini guda a Kano domin horas da ’yan jarida kan gyaran Dokar ’Yan Sanda ta 2020.
Taron wanda ya gudana a ranar Talata 10 ga Fabrairu a dakin taro na Royal Residence, Lamido Crescent, Nassarawa GRA Kano. Ya haɗa da masu rahoto, editoci da masu shirya shirye-shirye daga kafafen watsa labarai daban-daban ciki har da Kakaki24 .
A gabatarwarta, Aisha Isa Yusuf ta yi bayani kan tanade-tanaden dokar yan sanda ta 2020, wanda ya hada da haramtawa ƴan Sanda rike wanda ake zargi na tsawon awanni 24 – 48.
Ta kuma ce dokar ta hana kama dangi a maimakon wanda ake zargi, tare da wajabta sanar da iyali da kuma hana azabtarwa ko wulakanci.
Sauran wadanda suka gabatar da maƙala sun hada da Mr. Aro Leonard da Mr. Odoh Okenyodo wadanda suka yi bayani kan rawar da aikin jarida zai taka wajen wayar wa da alumma kai kan mafita wajen ƙarfafa amincewa tsakanin jama’ar gari da ƴansanda.
