Addini
An Ga Watan Azumin Ramadan a Saudiyya
Ƙasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan na shekarar 1447 Hijriyyah, lamarin da ke tabbatar da fara aazumi a hukumance.
Sanarwar ta fito ne ta hannun shafin Inside Haramain, wanda ke kula da yaɗa bayanai kan Masallatai Biyu Masu Daraja, inda ya bayyana cewa an ga watan ne a yau Talata.
Wannan na nufin al’ummar Musulmi a Saudiyya za su fara azumin watan Ramadan daga gobe Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026, wanda ke zama farkon watan ibada mafi muhimmanci a Musulunci.
