Addini
Ramadan: Gwamnatin Kano Ta Bayar da Umarnin Rufe Gidajen Tarukan Biki (Event centers) a Fadin Jihar
Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano State ta ba da umarnin rufe dukkan cibiyoyin nishaɗi da wuraren gudanar da bukukuwa, ciki har da gidajen gala da masu sana’ar DJ, domin bai wa al’umma damar gudanar da ibadar watan Ramadan cikin natsuwa. Hukumar ta ce umarnin zai fara aiki daga ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 10 na dare.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, ya bayyana cewa za a ci gaba da rufe wuraren har zuwa ƙarshen watan Ramadan. Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa musulmi sun samu yanayi mai kyau domin azumi da sauran ayyukan ibada ba tare da wata hayaniya ba.
Hukumar ta kuma buƙaci masu ruwa da tsaki su bi umarnin ba tare da saɓawa ba, tana mai cewa wannan na daga cikin aikinta na tabbatar da bin dokokin nishaɗi a jihar. Ta kuma yi addu’ar Allah Ya ba kowa damar kammala watan Ramadan cikin zaman lafiya da albarka.
