Featured
Egbetokun Ya Sauka Daga Muƙamin Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya
Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya sauka daga muƙaminsa, kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta shaida wa BBC. Majiyar ta ce ya ajiye aikin ne a ranar Talata, sai dai ba a fitar da sanarwa a hukumance ba kan matakin.
Har zuwa yanzu rundunar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ba ta bayyana matsayarta a hukumance ba dangane da saukar tasa. Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan makomar shugabancin rundunar.
Sai dai babu cikakken bayani a hukumance da ke bayyana dalilin da ya sa ya ajiye aikin. Lamarin ya janyo hankulan jama’a musamman ganin matsayin da yake riƙe da shi a rundunar.
A watan Yunin 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya sanar da shi a matsayin wanda yake son naɗawa muƙamin. Daga bisani kuma Majalisar ‘yan sandan ƙasar ta tabbatar da naɗin nasa a ƙarshen watan Oktoban 2023.
