Featured
Bom Ya Tarwatsa Motar Siminti a Hanyar Gusau zuwa Funtua
Wata nakiya da ake zargin ‘yan bindiga ne suka dasa ta fashe da wata motar tirela ɗauke da siminti a babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a jihar Zamfara. Lamarin ya haddasa cunkoson ababen hawa na wani lokaci kafin daga bisani aka samu sauƙi.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Yazid Abubakar, ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin. Ya ce suna zargin ‘yan bindiga ne suka dasa abin fashewar, amma bincike na ci gaba, yana mai cewa babu wanda ya rasa rai kuma jami’an tsaro sun tsare yankin.
Fashewar ta faru ne a ƙauyen Unguwar Mai Chida da ke ƙaramar hukumar Tsafe lokacin da motar ke tafiya daga Sokoto zuwa Kaduna. duk da motar ta lalalce sosai amma babu asarar rai, sai dai ana ci gaba da fuskantar irin waɗannan hare-hare a jihar.
