Featured
Ministoci 2 Sun Yi Murabus Domin Tsayawa Takarar Zaɓe a 2027
Ministocin harkokin waje, Yusuf Tuggar, da karamin ministan jin ƙai, Yusuf Sununu, sun yi murabus daga mukamansu domin tsayawa takarar zaɓe a shekarar 2027. Matakin ya biyo bayan umarnin gwamnati da ya tilasta duk masu muƙaman siyasa su sauka kafin ranar 31 ga Maris, 2026 idan suna da niyyar tsayawa takara.
Rahotanni sun nuna cewa Tuggar ya yi murabus ne domin neman kujerar gwamnan jihar Bauchi, yayin da Sununu ke shirin tsayawa takarar sanatan Kebbi. Doka ta tanadi cewa dole ne duk masu riƙe da muƙaman gwamnati su sauka kafin shiga zaɓen fidda gwani, domin kauce wa amfani da iko ko dukiyar gwamnati wajen neman rinjaye.
Baya ga ministocin biyu, wasu manyan jami’an gwamnati sun fara ajiye mukamansu, ciki har da Nasiru Gawuna da Abdulrazak Namdas. Ana sa ran ƙarin murabus daga wasu ministoci da shugabannin hukumomi yayin da wa’adin ke cika, lamarin da zai iya haifar da sauye-sauye a majalisar zartarwa ta tarayya nan gaba kaɗan.
