Featured
Rikicin Gabas Ta Tsakiya Na Iya Haifar da Tashin Farashin Taki a Najeriya
Masu hada taki a Najeriya sun gargadi manoma cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya janyo tashin farashin taki, wanda hakan zai ƙara tsadar noma da kuma rage yawan amfanin gona a ƙasar.
Shugaban ƙungiyar masu hada taki, Abubakar Kassim, ya ce sun riga sun shirya tsaf domin kakar noman bana tare da wadataccen kayan aiki, amma ya amince cewa rikicin duniya ya fara tasiri kan farashi. Ya ce idan rikicin ya ɗauki lokaci, farashin taki zai ci gaba da tashi yayin da kakar noma ke ƙaratowa.
A gefe guda, gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti ƙarƙashin mataimakin shugaban ƙasa domin duba yadda rikicin zai shafi noma da kuma nemo hanyoyin rage tasirinsa. Haka kuma masana sun bukaci gwamnati ta dawo da tallafin taki domin sauƙaƙa wa manoma da kuma hana tashin farashin abinci.
