Featured
Kano : Hukumar Kula da Harkokin Shari’a Ta Musanta Rahoton Wanke Murtala Garo Daga Zargin Rashawa
Hukumar shari’a ta Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke yawo cewa wata kotu ta zauna kwanan nan ta wanke tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo daga zargin rashawa. Hukumar ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya, tana mai cewa babu irin wannan zaman kotu da aka gudanar a halin yanzu.
Hukumar ta ƙara da cewa labarin da ake yaɗawa na da alaƙa da wata tsohuwar shari’a da aka yi a shekarar da ta gabata, ba sabuwar shari’a ba. Haka kuma ta jaddada cewa alkalan da rahoton yace sun yanke hukunci a halin yanzu ma suna cikin hutu ne, wanda ya sa ba zai yiwu a ce an gudanar da zaman kotu a wannan lokaci ba.
Wannan bayani ya zo ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce da jan hankali kan al’amuran shari’a da siyasa a Kano, musamman dangane da batun Garo da ke ci gaba da jan hankalin jama’a.
