Featured
NEMA Ta Gargaɗi Jihohi 30 Kan Yiwuwar Samun Ambaliyar Ruwa
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, National Emergency Management Agency ta yi kira ga gwamnonin jihohi da su fara ɗaukan matakan rigakafi domin kauce wa matsalar ambaliya a daminar bana. Hukumar ta ce fiye da jihohi 30 na iya fuskantar matsananciyar ambaliya.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, shugabar hukumar, Zubaida Umar ta buƙaci jihohin da su gaggauta ɗaukar matakai domin rage illar ambaliyar da aka yi hasashen za ta afku a wasu sassan ƙasar.
Sanarwar ta ce matakan da ake sa ran jihohin za su ɗauka sun haɗa da farfaɗo da tsaftar muhalli akai-akai da kuma gyaran magudanan ruwa. Haka kuma ta yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini da ƙungiyoyin matasa da kafafen yaɗa labarai su mara wa ƙoƙarin hukumar baya.
