Featured
Dole Ne a Hana Gwamnoni Iko da Ƴansandan Jihohi – Dambazau
Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida kuma tsohon hafsan sojin ƙasa, Abdulrahman Dambazau ya ce kafa ’yan sandan jihohi ba zai yi tasiri a Najeriya ba sai an tabbatar da ƙwarewa da cikakken tsarin aiki mai inganci.
Dambazau ya bayyana cewa dole ne a hana gwamnoni iko kai tsaye a kan rundunar domin gudun amfani da ita wajen muzgunawa abokan hamayya na siyasa. Ya kuma buƙaci a tabbatar da tsauraran matakan tantancewa, horaswa da kuma kula da jami’an domin hana cin zarafi da tabbatar da bin doka da kare haƙƙin ɗan Adam.
Tsohon hafsan sojin ya ce matsalar tsaro ta fi ƙamari ne a yankunan karkara inda babu isasshen jami’an tsaro, abin da ke sa ake kira da a kafa ’yan sandan jihohi. Sai dai ya jaddada cewa dole jihohi su samar da isasshen kuɗaɗe, kayan aiki da walwalar jami’ai tare da gina amincewa tsakanin jama’a da jami’an tsaro domin tsarin ya yi nasara.
