Featured
APC 2027: Tuggar Da Wunti Sun Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin Takarar Gwamna a Bauchi
Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, da Bala Maijama’a A. Wunti, tsohon babban jami’in NNPC Limited, sun sha kaye a zaben fidda gwanin takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar All Progressives Congress.
Rahotanni sun bayyana cewa an jinkirta sanar da sakamakon zaben da aka gudanar ranar Alhamis har zuwa safiyar Asabar, inda aka ayyana tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin.
Mohammed Abubakar, wanda aka fi sani da MA, ya taba rasa kujerar gwamnan jihar a shekarar 2019 bayan ya sha kaye a hannun Bala Mohammed na jam’iyyar PDP. Yusuf Tuggar kuwa na daga cikin ministocin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da suka sauka daga mukamansu domin neman takara a babban zaben shekarar 2027.
