Featured
Akwai Yiwuwar Tashin Farashin Gas Ɗin Girki a Najeriya
Ana ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar ƙarin tashin farashin gas na girki a Najeriya, yayin da ’yan kasuwa da masu amfani da shi ke fama da matsin lambar tsadar rayuwa da hauhawar farashi a sassan ƙasar.
Ƙungiyar Nigeria Association of Liquefied Petroleum Gas Marketers ta bayyana cewa ƙarancin wadata da tsadar gas a tashoshi, tare da matsalolin sufuri da ƙarin kuɗaɗen gudanar da kasuwanci, na daga cikin abubuwan da suka haddasa hauhawar farashin gas daga naira 1,300 zuwa kusan naira 1,500 kan kilo guda a wasu yankuna.
Ƙungiyar ta ce ’yan kasuwa na sayen tan 20 na gas kan fiye da naira miliyan 25 zuwa 26, lamarin da ke ƙara ɗora wa masu amfani nauyi a kasuwa. Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa rashin ɗaukar matakan gaggawa na iya ƙara jefa gidaje da ƙananan kasuwanci cikin wahala tare da haddasa ƙarin tashin farashin abinci a ƙasar.
