Featured
Jami’an Tsaro Sun Dakatar da Hawan Sallah a Kano
Hukumomin tsaro a jihar Kano sun dakatar da gudanar da Hawan Sallah domin kaucewa yiwuwar rikici da barazanar tsaro da ka iya tasowa a lokacin bukukuwan Sallah. Matakin ya biyo bayan fargabar gudanar da hawan sallah daga bangarori biyu masu ikirarin sarautar Kano.
Tun da farko, Muhammadu Sanusi II ya shirya gudanar da Hawan Daushe bayan hawan idi, yayin da shi ma Aminu Ado Bayero ya bayyana aniyarsa ta gudanar da irin wannan hawa. Lamarin ya janyo fargabar cewa haduwar magoya bayan bangarorin biyu na iya haddasa tashin hankali a birnin Kano.
Sai dai bayan umarnin da jami’an tsaro suka bayar, bangarorin biyu sun amince da dakatar da Hawan Daushe domin tabbatar da zaman lafiya a jihar. Hukumomin sun ce matakin na daga cikin kokarin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma yayin bukukuwan Sallah.
