Featured
Da Amincewata Aka Ba Wa Gawuna Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya – Sanata Rufa’i Hanga
Sanata Rufa’i Hanga ya bayyana cewa babu wani abu da zai iya raba shi da jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
A wata hira da ya yi ta wayar tarho da manema labarai, Hanga ya ce da amincewarsa aka bai wa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Ya kuma jaddada cewa babu wata matsala a cikin Kwankwasiyya, yana mai bayyana Kwankwaso a matsayin mutum mai adalci. Hanga ya ƙara da cewa a shirye yake ya tunkari duk wata fitina da za ta taso wa Kwankwaso da Kwankwasiyya.
