Featured
Gwamna Kano Ya Haɗe Ma’aikatun Ruwa Da Muhalli Zuwa Ma’aikata Guda Ɗaya
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da haɗe Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi zuwa ma’aikata guda ɗaya mai suna Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi.
Wata takarda da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar F. Ibrahim, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin ƙara inganta gudanarwa, haɗa manufofi da kuma amfani da albarkatu yadda ya kamata wajen kula da harkokin ruwa da muhalli a jihar.
Sabuwar ma’aikatar za ta gudanar da ayyukanta ta hanyar daraktoci biyu, wato Daraktan Albarkatun Ruwa da Daraktan Muhalli da Sauyin Yanayi. Takardar ta ce sabon tsarin zai fara aiki nan take, tare da umartar dukkan hukumomi da sassan da abin ya shafa su daidaita ayyukansu da sabon tsari.
