Featured
Gwamnatin Kano Ta Bai Wa ’Yan Kwangila Wa’adin Watanni 8 Domin Magance Matsalar Ruwan Sha a Jihar
Gwamnatin Jihar Kano ta bai wa kamfanonin da ke gudanar da ayyukan gyara da inganta hanyoyin samar da ruwa wa’adin watanni takwas domin kammala ayyukan da ake sa ran za su taimaka wajen magance matsalar ƙarancin ruwa a faɗin jihar.
Mukaddashin Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jihar, Dahiru M. Hashim, ne ya bayyana hakan yayin da yake duba ci gaban aikin gyaran babbar ma’ajiyar ruwan Goron Dutse, wadda ita ce muhimmiyar cibiyar rarraba ruwa ga mazauna Kano.
A cewarsa, aikin ya haɗa da gyaran tankunan ruwa da suka lalace tun shekaru da dama da suka gabata, sauya bututu da kuma cire laka daga manyan tankuna. Ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta himmatu wajen tabbatar da wadataccen ruwa mai tsafta, tare da jaddada cewa ba za a amince da jinkirin kammala ayyukan ba.
