Featured
Kwankwaso Ya Musanta Zargin Shirya Zanga-Zanga Kan Matsalar Tsaro a Najeriya
Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin gudanar da zanga-zanga kan matsalar tsaro da ke ƙara ƙamari a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Kwankwaso ya bayyana saƙon a matsayin ƙarya da yaudara, yana mai gargadin jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba su da tushe.
Ya jaddada cewa shi da jam’iyyarsa ba sa goyon bayan duk wani mataki da zai iya haddasa rikici ko lalata rayuka da dukiyoyi. Ya ƙara da cewa suna da yaƙinin samun nasara ta hanyar zaɓe, yana mai kira ga jama’a su yi watsi da saƙon da ake yaɗawa.
