Addini
Auren Gata: Gwamnatin Kano Ta Sanya Ranar Aurar Da Mutum 1,500
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa za a gudanar da auren mutum 1,500 da za su ci gajiyar shirin auren gata daga ranar 6 zuwa 9 ga watan Agustan 2026. Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan.
Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da fitar da Naira biliyan 1.5 domin gudanar da shirin. A ranar 6 ga Agusta za a ba da shawarwari, ranar 7 kuma za a ɗaura auren, sai walima a ranar 8, kafin a raba kayan tallafi a ranar 9 ga watan.
Read Also : Rundunar Sojin Najeriya Na Neman Wani Soja Kan Zargin Sayarwa da Ƴanbindiga Kakin Soji
Shirin ya tanadi tallafi ga marasa galihu, zawarawa da masu ƙaramin ƙarfi. Kowace amarya za ta samu Naira 100,000 domin fara sana’a, yayin da kowane ango zai samu Naira 100,000 don taimaka masa wajen biyan sadaki, baya ga kayan ɗaki da kayan abinci.
Hisbah ta ce sama da mutum 5,000 ne suka nemi shiga shirin, amma mutum 3,000 aka tantance bayan gwaje-gwajen lafiya. Hukumar ta kuma gargaɗi jama’a da kada su biya kuɗi domin shiga shirin, tare da jaddada cewa gwamnatin jihar ce ke ɗaukar nauyin sa gaba ɗaya.
