Addini
Zaɓen 2027 : Ni ba ɗan siyasa bane, don haka babu ɗan takarar da zan yi wa yakin neman zaɓe – Daurawa
Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Malam Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce shi ba ɗan siyasa ba ne kuma ba zai yi wa wani ɗan takara yaƙin neman zaɓe ba a babban zaɓen 2027.
A baya-bayan nan ne aka sanya sunansa tare da tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Pakistan, cikin kwamitin ba da shawara kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna na jam’iyyar APC a Kano.
Read Also : Yobe Assembly Approve The Establiment Of State Police Service, 25 Others Bills
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, Daurawa ya ce burinsa shi ne Allah Ya bai wa duk wanda zai yi adalci, ya tausaya wa talakawa, ya kare haƙƙoƙinsu kuma ya inganta rayuwarsu nasara.
Daurawa ya ce: “Ni ba ɗan siyasa ba ne kuma ba zan yi wa kowa kamfen ba.” Ya kuma roƙi Allah Ya ba ƙasar shugabanni masu gaskiya, riƙon amana da tsoron Allah, waɗanda za su fifita muradun al’umma.

Pingback: Ba don Tinubu ba, da Buhari ba zai samu shugaban Najeriya ba - Shettima - KAKAKI 24