Featured
250,000 Ya Kamata Sojoji Su Riƙa Karɓa a Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi – John Enenche
Tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche (mai ritaya), ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara albashin sojojin Najeriya, inda ya ce bai kamata soja ya riƙa karɓar ƙasa da Naira 250,000 a duk wata ba.
Enenche ya bayyana hakan ne bayan Ministan Tsaro ya ce an ƙara mafi ƙarancin albashin sojoji daga Naira 49,000 zuwa Naira 100,000. Ya ce duk da ƙarin, albashin har yanzu bai dace da halin tsadar rayuwa da irin sadaukarwar da aikin soja ke buƙata ba.
Read Also : Auren Gata: Gwamnatin Kano Ta Sanya Ranar Aurar Da Mutum 1,500
Ya ce Naira 250,000 ma ba shi da yawa idan aka yi la’akari da kuɗin abinci, sufuri da sauran buƙatun rayuwa. Ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa gidaje da kayan aiki da gwamnati ke ba sojoji sun isa su maye gurbin albashi mai kyau.
Tsohon Janar ɗin ya jaddada cewa sojoji ba sa samun damar yin wata sana’a ta gefe saboda yanayin aikinsu, yana mai cewa inganta jin daɗinsu zai ƙara musu ƙwarin gwiwa da inganta yaƙi da matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
