Featured
Masu Garkuwa Sun Sace Ƙanwar Tsohon Ministan Lantarki Da Ƴaƴanta a Ibadan
Wasu mutane dauke da makamai sun yi garkuwa da Olaide Busayo Adegoke John-Paul, ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki Adebayo Adelabu, tare da ‘ya’yanta tagwaye Peter da Paul a safiyar Laraba a yankin Challenge da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
A cewar iyalan Adelabu, an sace matar mai shekaru 43 ne da misalin ƙarfe 7:30 na safe yayin da take kan hanyarta ta kai ‘ya’yanta makaranta. Sun bayyana cewa an sanar da jami’an tsaro nan take, kuma an fara bincike tare da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace da kuma kamo masu laifin.
Iyalan sun ce suna da yakinin cewa hukumomin tsaro za su yi nasarar kubutar da matar da ‘ya’yanta cikin ƙoshin lafiya, tare da roƙon jama’a su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba. Kakaki24 ta ruwaito cewa lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a wasu sassan Jihar Oyo.
